Babbar kotu a birnin tarrayar Nijeriya Abuja, ta dakatar da shugaban jam’iyar APC Adams Oshiomhole daga matsayinsa na shugaban jam’iyar.

Mai shari’a Ɗanlami Senchi, ne ya sanar da hakan ranar Talata, in da ya bukaci Oshiomhole, ya sauka daga mukaminsa sakamakon karar da aka shigar gaban kotun don yunkurin tsige shi daga mukaminsa.

Rigima ta ɓarke cikin jam’iyar abin da ke nuna shirye-shiryen neman takara a 2023 na kara yin sama.

Jam’iyar ta daɗe tana tana fama da rikici kan shugabanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *