Spread the love

 APC har yanzu ba ta samu bayani a rubuce ga ɗan takararsu da ya janye ba

Shugaban jam’iyar APC na Sokoto Alhaji Isah Sadik Acida ya ce har yanzu ɗan takararsu da ya janye a zaɓen cike gurbi da hukumar zaɓe za ta gudanar ran 14 ga watan maris 2020 bai sanar da su a rubuce ba, don haka ba zai cewa komi ba a lokacin da managarciya ta nemi jin ta bakinsa.

Ɗan takarar na jam’iyar APC Abubakar Bello Umar, ya janye takararsa da ƙashin kansa.

A tabakin Umar ya janye ne domin samun haɗin kai da cigaban ƙaramar hukumar ta Keɓɓe, kan haka ya janye duk wata takararsa.

Ya ce kafin haka sai da yayi shawara da mahaifansa da yannensa da sa’o’insa da abokai da masu fatan alheri dukansu sun cimma matsaya ya janye takarar.

Wannan matakin ya zo wa magoya bayan jam’iyar APC da mamaki ganin yanda ɗan takarar ya janye sati ɗaya kafin gudanar da zaɓe, a yankin da jam’iyarsu ke da ƙarfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *