Spread the love

Gwamnatin jihar Sokoto za ta kwaikwayi tsarin bayar da ilmin zamani na kasar Indonesia don musanya tsarin Almajiri da ake da shi a jiha.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da hakan a ranar lahadi lokacin da yake karbar jekadan kasar Indonesiya a Nijeriya AVM Usra Hendra Haraha da ya kawo masa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jiha.

Tambuwal ya ce zai tuntubi Sarkin Musulmi da duk wasu masu ruwa da tsaki domin a yi tafiya tare domin jihar Sokoto ba ta gaggawa a lamarin kamar yadda wasu jihohi suka yi suka kashe tsarin almajiri ba tare da sun kawo wata mafita ba.

Ya nuna gamsuwarsa tsarin da za su kwaikwaya na kasar Indonesiya zai iya zama mafita ga sauya tsarin almajiri.

A bayanin da mai baiwa gwamnan Sokoto shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya fitar ya ce gwamnan ya jinjinawa kasar Indonesiya kan amincewarta ga turo kwararri domin kara ilmi ga jihar a fannin tattalin arziki.

Jekadan ya ce ya ziyarci Sokoto don kara inganta hulda ta musamman a fannin ilmi da aikin noma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *