Spread the love

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto

Kwamitin Lamurran addinin Musulunci na Majalisar dokokin  jihar sokoto a cigaba da rangadin gani da ido a ma’aikatu  da hukumomin da ke Karkashin kulawarsu,   sun kai ziyara a hukumar Zakka da wakafi karkashin jagorancin Shugaban kwamitin Honarabul  Abubakar Shehu Yabo,  ya  bayyana anniyarsu ta goyon bayan hukumar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso

Shugaban kwamitin ya yabawa gwamnan jiha Aminu Waziri Tambuwal a kan goyon bayan da yake baiwa hukumar.

Shugaban Hukumar zakka da wakafi ta jihar Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato, yayi bayanin irin dinbin ayukkan da hukumar ta aiwatar, da kalubalen da hukumar ke fuskanta.

Shugaban ya nemi hadin kan Majalisar dan hada hannu a yi wa addini da al’umma aiki. 

Daga bisani an kai ziyara wurin da Gidauniya Qatar ke gina cibiyar musulunci Wadda wata mata ta hannun cibiyar ba da tallafin ta kasar Qatar ke yi babu irinta a duk fadin kasar nan  mai dauke  da Gidajen kwana, makaranta, wurin tarbiyya, gidan Biredi, wurin kashe Gobara da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *