Spread the love

Jaruma Hafsat Idris wadda aka fi sani da Ɓarauniya da jaruma Fati Abdullahi wadda aka fi sani da Washa za ka iya bayyanasu da cewa sun fi sauran jarummai mata dake cikin masana’antar shirya finafinnai samun sa’a a Kano.

Suna jan zarensu a yanzu sun mallaki motocin kece reni na alfarma, sun mallaki gidaje da filaye a jihohin Kano da Kaduna da Sokoto, ga kuma kuɗaɗe maƙare a asusun ajiyarsu na banki kamar yadda jaridar blueprint ta kawo.

Duk da haka dukkan waɗan nan ‘yan wasan suna da abin da ya zamar musu cikas da suke son cike giɓinsa.

Akwanakin nan suka karaɗe tuarakarsu ta facebook da Instagram suna shelanta sun matsu suna son su yi aure. Ba tare da sun sanya wani sharaɗi ba.

Fati Washa dake zaune a Kwatas na Kinkinu a Kaduna tare mahaifanta cikin wani danƙareren gida da ta saya musu.

Fati Washa wadda sikandari kawai ta kammala ta samu nasara a rayuwarta.

A wani hannun kuma Hafsat Idris bafullatana ce daga Sokoto ta taɓa yin aure shekara tara in da ta haifi yara huɗu kafin ta rabu da mijinta, a masana’antar shirya fim ta samu laƙabin Ɓarauniya a fim da ta yi tare da Ali Nuhu.

Lokacin ta zama mai zafi a masana’antar ta riƙa tashe a kwanan ma ta samu wata kwangila da kamfanin mai na Delfin in da za su yi amfani da hotonta a talla za su biyata miliyan 30.

Fati ana yaɗa jitajitar tana soyayya da jarumi Nuhu Abdullahi, ta saka hotonta tana addu’ar Allah ya ba ta miji nagari ba ta son mai kudi domin ita tana da abinta.

Dukkansu suna son yin aure bayan nasarar rayuwa da suka samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *