Spread the love


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari shawara ta mayar da hankali tare da zage damtse wurin ɗaukan mataki kan Coronavirus.
 

An samu ɓullar cutar na farko ne a jihar Legas a ranar Alhamis, yayin da an samu ɓullar cutar a wasu kasashen duniya 12 cikin sa’o’i 48.
 

A sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, Atiku ya ce ya zama dole Najeriya ta ɗauki matakai irin waɗanda ta ɗauka yayin ɓullar cutar Ebola.
 Ya ce, “Ya zama dole mu tuna yadda muka yaƙi Ebola inda muka zama ƙasa na farko a duniya da ta ci galaba a kan mummunar cutar a shekarar 2014.

Yaya Najeriya ta cimma wannan nasarar? Mun cimma nasarar ne ta hanyar haɗin kai.
 “Ya zama dole gwamnati mai ci yanzu ta yi aiki tare da gwamnatocin jihohin Legas da Rivers. An samu cikakken haɗin kai da aiki tare wadda hakan ne ya bayar da damar cin galaba a kan cutar mai kisa.” 

Wazirin Adamawan ya kuma bayar da shawarar cewa yanzu ba lokaci ba ne na nuna ɗan yatsa.
 

Atiku ya bayyana cewa Najeriya na bukatar ɗaukan matakai kwarara domin kare afkuwar yaɗuwar cutar.
 

“A baya-bayannan, mun rufe iyakokin kasar mu saboda kare tabarbarewar tattali arziki. Yanzu lokaci ne da za a dakatar da jirage masu tashi da shigowa kasar duba da yaduwar da cutar ke yi. 


“Ɗan takarar shugaban kasar na PDP a shekarar 2019 ya kuma shawarci a samar da na’urorin gwajin cutar a filayen jiragen saman mu.

“Abinda ya fi muhimmanci, kada ‘yan Najeriya su firgita.


 Al’umma da gwamnati duk sun haɗa kai sun kawar da Ebola a baya, kuma yanzu shima za mu iya kawar da wannan annobar,” in ji mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *