Spread the love

Ta je barbara ta dawo da ciki!  Wajen kwaliya da son a birgewa  ne ta mayar da kanta makauniya. 

Ta kai kanta  wajen masu rina kwayar ido amma sai aka yi rashin sa’a ta zama makauniya. 

Yarinya mai suna Aleksandra Sadowska ‘yar asalin birnin Wroclaw ce a yammacin kasar Poland mai shekaru 25 a wajen rina kwayar idonta ne ta zama makauniya.

Ta so yin koyi da mawakin gambara mai suna Popek ne wanda ya rina kwayar idon shi zuwa baki.

Bayan an gama bin duk wasu hanyoyin da suka dace don mayar da kwayar idon baki gaba daya, Aleksandra ta fara korafin ciwon ido amma sai mai rina idon ya ce mata kada ta damu, ya shawarceta da ta sha maganin kashe zafin ciwo.

An yi rashin sa’a da aka gama kwalliyar ta daina gani kwata-kwata, likitoci sun sanar da budurwar cewa ba za ta taba warkewa ba kuma idonta na hagu zai daina gani nan ba da dadewa ba, bayan tafiyar na daman.

Tuni dai aka damke wanda yayi mata aiki a idon mai suna Piotr A, an yanke masa hukuncin zai kwashe shekaru uku a gidan yari sakamakon makantar da ita da yayi ba da gangan ba.

A yayin da aka ci gaba da bincike kan lamarin, an gano cewa wanda yayi mata aikin idon ya yi kura-kurai masu tarin yawa a yayin yi mata aikin. Ya yi amfani da ruwan rinin da ake yi wa jiki wanda kuma ba a so ya taba ido kwata-kwata.

Lauyan budurwar ya sanar da kafafen yada labarai cewa: “A bayyane yake idan aka ce mai aikin idon bai san yadda ake yi ba. Haka kuma ya dage wajen jefa rayuwar budurwar cikin mugun hali.”

Aleksandra ta ce: “Wannan abu bai yi dadi ba. A halin yanzu dai likitoci ba su bani karfin guiwar jin sauki ba, an yi min illa babba. Ina tsoron zan makance duka. Ba zan rufe kaina a gida in ci gaba da fama da bacin rai ba. Dole ne in fito in ci gaba da rayuwa.” a cewarta.

Wannan halin da ya samu wannan baiwar Allah wata izna ce ga mata masu son yin kwalliya a cikin idonsu ta sanya wani abu wanda asali bako ne a wurin ido da sunan kwalliya, yakamata mata a wannan zamani su yi karatun ta natsu su guji sanyawa idonsu kowane abu da sunan kwalliya in ba kwalli ne da masana kiyon lafiyar ido suka aminta yana taimakon lafiyar ido da gani, don su kaucewa jawowa kansu abin da ya fi zare tsawo.

Majiya: Gaskiya dokin karfe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *