PDP ta jingine maganar neman sake duba hukuncin shugaban kasa a kotun koli

Taron gaggawa na shugabannin zartarwar jam’iyar PDP karo na 89 a jiya Alhamis ya kasa umartar shugabannin gudanarwar jam’iyar kan su je su gabatar da korafin neman sake duba hukuncin shugaban kasa da kotun koli ta aiwatar a watannin da suka gabata.

Bayan da shugabannin gudanarwar PDP suka fitar da bayanin za su nemi kotun koli ta sake duba hukuncin nata ‘yan Nijeriya sun zuba ido su ga lokacin da za a sanya korafin da sakamakon hukuncin da korafin zai samo, sai ga shi abu ya tsaya cik, abin da wasu ke ganin bai rasa nasaba da hukuncin jihar Bayelsa da kotun koli ta zartar a satin nan.

A kwanakin da suka wuce Sakataren yada labarai na jam’iyar Kola Ologbondiyan ya sanarwa manema labarai a Abuja cewa biyo bayan jam’iyar APC ta koma kotun koli domin duba mata hukuncin jihohin Bayelsa da Zamfara, hakan ya sanya PDP za ta nemi a duba mata hukuncin shugaban kasa.

Shugabanin zartarwar jam’iyar su ne na biyo ga yanke hukunci bayan shugabannin gudarwa sun zartar da hukunci, a wannan lamarin ba su bayar da damar sanya neman duba hukuncin ba, kasa ba da umarnin ana ganin yana da nasaba da hujjojin da ake da su na hukuncin na bukatar duba su a tsanake.

Jam’iyar ta kaddamar da kwamitin mutum 14 da zai duba abubuwan da suka faru a zaben 2019.

A jawabinsa ga manema labarai bayan kare zaman da ya share awa biyu ana gudanar da shi Sakataren jam’iya Kola ya ce jam’iya ta aminta da a sanya gaba kan abubuwan da suka shafi zabe da rike ingantattun hujjoji.

Ya ki karba tambayar da aka yi masa na yaushe ne za su gabatar da korafin sake dubu hukunci a kotun koli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *