Spread the love

Shin ka San Menene Stigma a Hausance? Stigma kalma ce ta turanci da ake amfani da ita Wanda idan zaka fassara da Hausa Kai tsaye sai ka ce, Jefa tsoro a cikin mutum domin ya hana shi bacci.

Wannan Kai tsaye shi ne abin da na Sani game da wannan kalma ta Stigma, Amma me ya hada wannan kalma da bayanin da nake so nayi?

Saurara

Yau yau dinnan hukumar lafiya ta hannun ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ta bayyana cewa, An samu bullar cutar Corona Verus a Nigeriya.

Corona suka ce na daga cikin manyan Kwayoyin cuta da ba a Ganinsu da ake dauka daga dabbobi wacce ke kawo Marsala ta jin matsanancin sanyi a jiki har ta shafi huhun Jikin mutum Dan Adam kuma Ita wannan cuta takan yadu tsakanin mutum da mutum. Kuma yaduwarta kamar an cilla bindiga ne (Domin KO ta hanyar shakar numfashi zata iya Kama mutum). Wannan kenan sai Ku nemi likitoci domin jin karin bayani.

To meyasa wannan Abin zai zama barazana KO tsoratarwa ga Musulmi?

A Shekaru masu Yawan Gaske a Wani zama da Yahudawa suka yi a Germany karkashin shugaban Germany na wancen lokaci Bismarck suka ce, Makawar kuna bari musulmi na taruwa domin yin aikin hajji to kuma zaku rasa bartabarku domin duniya duka zasu dauka musulmi sun fi yawa (kuma wannan ba karamar Matsala ba ce), domin za su rika jan sauran addinai suna shiga musulunci.

Kafin yin wannan bayani ina komawa ga wasu kudurori na Yahudawa da suka yi alkawarin gabatar da su ga musulmi. Domin daga cikin kudurukkansu akwai dakatar da musulmi daga zuwa aikin hajji da Umrah.

  • Mu dawo kan bayanin mu Meyasa wannan Cuta za ta zama Stigma ga Musulmi? Daga dakatarda Aikin Umra na dan lokaci da Kasar saudiya ta yi ga kasashen da ake tunanin suna da wannan Cutar da bayyana an samu bullar cutar a Iran da Najeriya duka duka baiyi awa 24 ba. Kai tsaye wannan zai hasko mana da bayanin zaman da yahudawa sukayi a Germany(hasashe).

Ka da rubutuna ya yi tsayi Kai tsaye ina son in ce ne Yahudawa da ‘yan korensu za su yi amfani da wannan cutar idan Allah bai tsare ba su sanya a hana zuwa saudiya ga kasashe da yawa na Musulmi.

Mu bama inkari da ɓullar Cutar kuma munyar da akwai ta Sai Dai muna cewa, wanda hakoransa basu da ƙarfi idan ya tashi cin ƙashi to yayi a hankali.

Wannan Kira ne ga ‘Yan Uwanmu marubuta musamman waɗan da ke yi da turanci dole ne mu ta shi tsaye mu tabbatar da gaskiyar wannan abin kuma mu bayyanawa duniya.

Ina Cewa, Innalillahi Wa Inna Ilaihin Raji’in

Jamilu Sani Rarah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *