Spread the love

Babbar kotun Ado Ekiti a jiya ta tura wani mutum Bashiru Adeyanju gidan yari shekara 14 saboda ya yi yunkurin yi wa ‘yarsa fyade mai shekara 17.

A lokacin da ta yanke hukunci mai shari’a Monisola Abdunde ba ta ba shi zabin biyan tara ba.

Monisola ta samu wanda ake zargi da laifin yunkurin yin fyade a bayanan da ya gabatar da shedun da aka kawo lokacin shari’ar.

Mai shari’a ta tabbatar da abubuwan da aka gabatar sun fito fili kan cewa ya yi yunkurin yin fyaden.

Ta ce kotu ta same shi da laifin da ya aikata, amma bisa ga rokon masu kariyarsa amatsayinsa wanda ake kara na farko kotu ta daure shi shekara 14 a gidan yari, shekara uku da ya yi a farko a hada da su.

Mai gabatar da kara wanda shi ne babban lauyan gwamnati ya ce wanda ake kara ya aikata laifin ne a 2017 a kan titin Irona birnin Ado Ekiti jihar Ekiti..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *