Kofura Soja dake aiki a karkashin rundunar sojan LAFIYA DOLE a babban sansani da aka tura a Malam Fatori a jihar Borno ya budewa abokan aikinsa wuta in da ya kashe mutum hudu ya raunata mutum biyu daga bisani ya kashe kansa.

Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na sojojin Col, Sagir Musa a bayanin da ya fitar ya ce lamarin ya faru a jiya da safe ne.

Musa ya ce jami’an da abin ya rutsa da su suna samun sauki a asibitin dake Maiduguri cikin babban birnin jihar.

Ya ce ananan ana kokarin ganin iyalan margayan su karbi hakkinsu na aiki, Allah ya gafartawa wadanda suka rasu.

Ya ce haka kuma bincike kan faruwar lamarin ana kansa domin sanin abin da ya hadasa hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *