Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal kuma shugaban gwamnonin jam’iyar PDP a Nijeriya  ya jagoranci zaman farko tun bayan zamansa shugaban Gwamnonin jam’iyar, taron ya gudana a gidan Shehu Shagari dake cikin gidan sauke baki mallakar jihar Sokoto a Unguwar Asokoro Abuja.

An samu halartar shugaban jam’iyar PDP Uche Secondus da gwamnonin jihohin Abia da Adamawa da Akwai Ibom da Bauchi da Bayelsa da kuma Delta, sai mataimakin Gwamnan Zamfara.

Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyar sun halarci zaman tare da wasu mambobin gudanarwar jam’iyar na kasa.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yana fuskantar babban kalubale a jam’iyar ta PDP ganin yanda aka daura masa nauyin jan ragamar kungiyar Gwamnonin jam’iyar domin ya samar da hadin kai a tsakaninsu gwamnoni, su yi tafiya tare da murya guda, abin da zai karawa jam’iyar farin jini da bunkasar samun magoya baya har ta kai ga karbar mulki a hannun jam’iyar APC a 2023.

Wannan nauyin da aka daura masa bisa zaton zai iya, ba karamin kalubale ne a wurinsa ba, ta la’akari da yanda tafiyar ta fara a zaman na farko bayan karbar jagorancin, a cikin gwamna 15 da jam’iyar ta ke da su 7 suka samu halarta a zaman farko da ya gudana in da gwamna 8 ba su halarta ba. Managarciya ba ta samu bayanan dalililan da suka hanawa sauran gwamnonin halartar taron farko na majalisar Gwamnonin ba.

Abin da ya sanya aka mayar da hankali ga zaman domin shi ne na farko anan ne ake yin tsarin abubuwan da za a sanya a gaba cikin shekaru masu zuwa, muhimmancinsa zai fi sauran domin shi ne taron farko da sabon shugaba zai ja goranta.

Duk yunkurin da managarciya ta yi domin magana da babban daraktan kungiyar gwamnonin jam’iyar PDP kan lamarin abin ya faskara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *