Spread the love

Hukumar sanya ido  ga harkokin  wutar lantarki na kasa  NERC ta haramta kamfanonin rarraba wutar lantarki(DISCOS) su 11 kada su cigaba da karban kudin wuta a kowane wata da ya wuce   naira dubu 1,800 daga abokan huldarsu a bangaren gidaje, har sai ta sa masu mita.

Sanarwar  umarni da hukumar ta fitar da ke dauke da sa hannun shugabanta farfesa James Momoh da kwamishininta a bangaren dokoki, tabbatar da bin ka’ida da kuma ba da lasisi Barista Dafe Akpeneye, hukumar ta NERC ta ce ta soke doka ta shekarar 2012 da ta baiwa kamfanonin damar sa kudin wuta kan tsarin kiyasi, sannan ta ce wannan dokar ya fara aiki tun a ranar Alhamis da ta gabata.

Hukumar ta ce adadin masu amfanin wutar lantarki a Nijeriya ya tashi daga miliyan 5 a shekarar 2012, zuwa miliyan 10 a watan Disamba ta shekarar 2019 da ta gabata.

Haka nan hukumar ta gargadi kamfanonin wutar da su samar da mita ga sauran rukunin abokan huldarsu, wadanda ba gidaje ba, kafin karshen watan Afirilu mai zuwa na sheakar 2020,  ta ce kwastomomin, na da zabin kin biyan kudin wuta idan ba a sa masu mita ba daga watan na Afirilu.

Wannan umarnin abu ne mai kyau da zai taimaki harkar kasuwancin wutar lantarki da za a yi nasarar kamfanonin su yi biyayya ga abin da hukumar ta fadi. Amma a halin kasar nan za ka samu a karshen wata mai kamawa kamfanonin za su iya yin biris da umarnin su fitar da Bill na kudin wuta su tsala kudin kamar yanda suka ga dama.

Managarciya na ba da shawara ga mutanen kasa su nemi hakkinsu matukar kamfanonin suka kasa bin umarnin wannan hukuma kan abin da ta umarce su da aiwatarwa, domin haka ne kawai zai taimaki aiki da doka a Nijeriya.

Kafin wannan dokar Kwastomomi suna koka yanda Kamfanonin ke tsala masu kudi yanda suka ga dama, ba tare da la’akari da hakikanin wutar da mutum ke ci ba, hakan zai ka ga mutum mai mita an daina daukar karatun mitarsa wanda ba ya da ita kuma kullum cikin bashin wuta yake wanda bai ci bai sha ba, kasuwancin wuta ba adalci da kwatantawa a cikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *