Spread the love

Kudirin dokar gyaran fuskar dokar kasa sashe na 308 na shekarar 1999, ya samar da rigar kariya ga shugabannin majalisa da suka kunshi shugaban majalisar dattijai da kakakin majalisar wakillai da mataimakansu da kakakin majalisar dokokin jihohi da mataimakansu, a jiya kuirin ya tsalke karatu na biyu a zauren majalisar wakillan Nijeriya.

Sashen na 308 dake cikin tsarin dokokin kasa shi ne ya samar da rigar kariya ga shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni da mataimakansu. A gyaran fuskar da ake son yi wa sashen ne ake son shigo da shugabannin majalisa na kasa da jihohi a sashen suma su amfana da kariyar da za ta hana su baiyana gaban kotu ko karba duk wata tuhuma har sai bayan wa’adin mulkinsu.

Manema labarai sun fahimci wannan ne karo na biyu a mulkin shugaba Buhari da ‘yan majalisa ke son kakaba wannan dokar, a majalisa ta takwas data gabata shugaban mara rinjaye a lokacin Leo Ogor ya gabatar da kudirin bai samu nasara ba.

Yanzu kuma dan majalisa Olesegun Odebunmi daga Oyo na jam’iyar APC ya fito da kudirin.

Shugaban masu rinjaye na majalisar ya aminta da kudirin ya ce kudirin dokar ba wai kan Kakin majalisar ba ne shi kadai ba kan zauren ne gaba daya.

Shugabannin farar hula a Nijeriya sun nuna rashin gamsuwarsu ga kudirin domin abu ne da zai kawo cigaban cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma. Suna ganin har rigar kariya da shugaban kasa da mataimakinsa da gwamna da mataimakinsa suke da ita yakamata a cire ta ba wai kara sanya wasu a rigar ba.

Farfesa Yadudu ya ce kudirin ba a yi shi domin al’umma ba sai don ‘yan majalisar su kadai.

Ya ce karara wannan rashin adalci ne da zai kara masu yin gaban kansu ga harkar wakilcin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *