Spread the love


Kotun ƙolin Nijetiya ta yi watsi da ƙarar da jam’iyar APC ta sanya na neman sake duba hukuncin da ta yi a 13 ga watan Fabarairun wannan shekara kan cire ɗan takararta David Lyon da mataimakinsa Degi da suka ci zaɓen gwamna a Bayelsa, amma kotu ta amshe kan matsalar takardun mataimakin dan takara.

A hukuncin da mai shari’a Amina Augie ta jagiranta kotun ƙoli ta umarci lauyoyin APC da Lyon su biya miliyan 10 kowanensu ga mutane uku da suke ƙara jimlar kuɗin miliyan 60 kenan.

APC ta tafi barbara ta dawo da ciki a wannan hukuncin da aka yanke mata, domin kotun ƙoli ba ta sake yin hukuncin da zartar domin masu ƙarar ba su da ingantacin hujjoji a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *