A wata takardar koke da Managarciya ta ci karo da ita a turakar facebook ta tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sokoto ta Arewa Alhaji Abdullahi Hassan wadda ya bayyana wasiƙa ce daga masu kishin jiha zuwa ga jagoran jam’iyar APC na jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, suna buƙatar ya ɗauki mataki a majalisar dattijai kan bashin biliyan 65.7 da gwamnatin Tambuwal za ta ciwo wa jihar Sokoto.

A bayanin sunce “Bisa dokar kasar mu ta Nigeria, akwai yanayi da adadin kudin da jihohi za su ciyo bashi Sai majalisar dattawa ta amince.”

“mu ‘yan jihar Sokoto masu nema cigabanta, muna rokon ka da ka duba wannan bukatar ta cin bashin da yakai ₦65.7 bisa adalci ga  alummar jihar Sokoto da kuma wadanda za su gabatar da bukatar.”

“ina tuna maka bashin da  aka ciwo baya ba mu gani a kasa ba, idan aka gabatar da na yanzu  a yi sharuddan da za’a kare gwamnatin jihar Sokoto mai zuwa da ‘ya’yan mu da  jikoki masu zuwa.”

“A sanya  sharadin da ba za’a wawushe kudaden ba idan ya zama tilas a karɓo bashin, idan ya kasance babu tillas a yi watsi da wannan bukatar.”

Wannan takardar tana baynin cewa gwamnatin jihar Sokoto ba ta da damar cin wannan bashin mai yawa haka sai majalisar dattijai ta ƙasa ta amince da karɓo bashin.

Abin jira a gani mataki na gaba da gwamnatin Sokoto za ta ɗauka kan karɓo bashin shi ne zai gasgnta bayanin masu takardar ko ya ƙarya ta su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *