Spread the love

Jam’iyar PDP ta yanke shawara za ta nemi kotun koli ta sake duba hukuncin da ta yanke kan zaben shugaban kasa da aka gudanar 2019.

A taron manema labarai da jam’iyar ta kira a yau Litinin a Abuja Sakataren yada labarai na jam’iyar Kola Ologbondiyan ya ce jam’iyar haka ma ta kamala shirin komawa kotun koli don ta nemi a sake duba hukuncin jihohin Osun da Kaduna da Katsina da Kano a hukuncin zaben gwamna da aka yanke.

A wannan lokacin ne a tarihin siyasar Nijeriya aka samu jam’iyyun da kotun koli ta yi wa ba dai-dai ba a wurinsu ke sake komawa domin ganin a gyara kuskuren da suke ganin an yi.

Wata mai kamawa ne kotun za ta duba wasu hukunci da aka sanya a gabanta domin sake gyaran kuskuren da ake ganin an tabka, daga lokacin ne za a iya gane an kuskuren hukunci ko dai bata lokaci ne kawai jam’iyyu suka kotu. Jam’iyar APC da PDP kowacensu na neman sake duba hukuncin da aka yanke a wasu jihohi daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *