Spread the love

Mahara sun nemi mutanen kauyen Akata a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina su biya harajin miliyan daya don tsiratar da kansu ga a kawo masu hari.

Wata majiyar da ta gayawa Daily trust mutanen kauyen sun fara karbar kudin da suka daurawa mutane kowane mutum zai biya 1500 don su cimma biyan bukatar maharan.

Kauyen Akata kamar sauran kauyukkan Batsari dake zagaye da maharan, wannan tashin hankalin ya fara sati biyu da suka wuce lokacin da wasu maharan suka zo kauyen suka saci shanu da wasu dabbobi.

Maharan sun nemi a basu miliyan daya amma mutanen gari sun cimma matsaya da su za su basu dubu 700 kan haka aka aje. kamar yadda wata majiya ta fadi.

Wata majiyar ta ce ‘yan sandan karamar hukumar sun yi kira ga mutanen su jefar da bukatar maharan amma ba su ji ba domin tsoron kar a kawo masu harin.

Jami’in hulda da ama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina SP Gambo Isah ya ce suna bincike, ba za su bar wannan abin haka ba, komi kankantar labari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *