Spread the love

  i 

Hukumar lura da ingancin abinci da magani a Nijeriya  NAFDAC ta gargadi ‘yan Nijeriya kan shan shayi a teburin masu sayar da shayi a waje  saman tebur.

Daraktar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta yi gargadin ne a wata hira da ta yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Abuja yau Litinin.

 Adeyeye ta ce gargadin ya zamo wajibi saboda an samu labarin cewa masu shayin sun fara gauraya  ruwan shayinsu da kwayoyi kafin baiwa masaya waton kwastamominsu.

Ta kawo misalin irin kwayoyin da ake sawa irinsu tramadol, Vieteling, Wiwi da Rapanol da sauransu. 

Ta kara da cewa mutane kan iya rasa rayukansu ko su kamu da wani mummunan ciwo idan aka gauraya shayi da wadannan muggan kwayoyin suka sha. 

Ta ce “A Amurka, mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar wadannan magungunan da ke bugarwa. Akwia magungunan da mutum ba zai sha ba idan yana fama da ciwon zuciya.“a cewarta. 

Hakazalika ta yi kira da yan Najeriya su guji shan magungunan kara karfin maza saboda illolinsu da suke tattare da shi, don kusan yanzu ana son mayarda shan maganin wani wajibi. 

A bangare guda, Kungiyar fafutukan dakile ta’amuli da muggan kwayoyi a Arewa wato Drug Free Arewa Movement, DFAM ta yi kira ga gwamnati ta haramta sana’ar sayar da magani a kafada ‘Kafada Kemist’ a dukan Arewacin Nijeriya domin magance shan kwayoyi ba bias ka’ida ba. 

Wata mambar kungiyar, Gambo Wakili, ta bayyana hakan ne yayinda take karanta jawabin da kungiyar ta saki bayan taron yaki da ta’amuli da kwayoyi cikin matasa da ya gudana a Abuja. 

Gambo ta ce ya zama wajibi a kawar da wadannan masu sayar da maganin saboda su ke sayarwa matasa magungunan da suke cutarsu.

 Ta yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa 19, da sarakunan gargajiya, ‘yan majalisa da masu ruwa da tsaki su sanya hannu wajen yakin magance kwaya da sace-sacen yara. 

A cewarta, lissafin da hukumar lissafi ta kasa wato NBS ta fitar kan ta’amuli da kwayoyi ya nuna cewa abin ya yi muni a Arewacin Najeriya.

Kan haka akwai bukatar daukar matakin gaggawa don fitar da matasanmu ga shiga halin rugujewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *