Spread the love

Shugaban hukumar Alhazzai ta Nijeriya Zikirullah Kunle Hassan ya nemi kwamitin su dubi yiwuwar rage kudin kujerar Hajji.

Shugaban ya nemi bukatar ne gare su a lokacin da yake kaddamar da kwamitin shi ne aikinsa na farko tun baya kama aiki.

Kwamitin ana sa ran su samar da wurin kwana da abinci ga mahajjatan 2020, kamar yadda bayani ke fadi wanda ya fito ta hannun mai kula da harkokin jama’a na hukumar Fatima Sanda Usara.

Ta ce shugaban ya yi kira ga mambobin su dauki aikin nan ba wasa ko wata banda kasa, su samar da wurin kwana da abinci masu kyau ga mahajjata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *