Spread the love


Wannan tambayar ta yi Matuƙar tayar min da hankali, tun a daren Jiya da Misalin ƙarfe 2 na dare, ina Sauraro da Kallon wasu karatuttuka da fatawoyi na Babban Malamin Hadeethin Nan dake ƙasar Masar Abu Isháq Al~Huwayniy (H)-, Daga Baya Hannuna Yakai Kan Wasu Baytukan Wáƙe Da Makarancin Qur’anin nan -Misháreey Al-Afasy (H), Wa’danda Yayi Musu Táke Da:-  “Kana Da Wani Sirri Tsakanin Ka Da Allah.???”.

Duk da na daɗe Ina Sauraron baitukan a Bakin Mutane, Shafukan Sàda Zumunta, Amma Jinta Da Kallonta Kai Tsaye Daga Bakinsa, Ya Matuƙar Girgizani, gaɓoɓin Jikina Duk Sukayi Sanyi, na maimaita Kallonta Ya Kai Kusan  Sau 10, Babbar Matsalar ita ce, na Kasa nemawa Kaina Amsar Tambayar Da Yake ta yi min a Waƙen nasa.
Akwai Wani Sirri Tsakanin Ka Da Allah…???!
Tambayar Da Ta ƙara faɗomin Kenan, ƙarfe 5 Na Asuba Bayan Na Farka Daga Barci, Domin Da Ita Na Kwana a Raina, Hawaye Ne Ya Cika Idanuna, Kunnuwana Suna Sauraron Harshena Kamar Daga Nesa Yana Ta maimaita Larabcin Waƙen, Yana ta tambayata,:-” Akwai Wani Sirri Tsakanin Ka Da Allah (Mahaliccinka).??!”
A Cikin Littafin Siyaru A’alamin Nubalá Na Gawurtaccen Malamin Nan, Shamsudden Azzahabiy (RH), A Cikin Volumes Mabanbanta, Gwargwadon Zamanin Da Yake Koro Tarihinsu a Cikin Volume ‘Din, Zakayi Ta Cin Karo Da Maganganu, Aiyukan Ibáda, Da Suka Ha’da Da Sadaqa, Karatun Qur’an, Kyautatawa Da Aiyuka Masu Tárin Yawa, Wanda Magabatan Wannan Al’ummah Suka Shahara Dasu, Kowanne a Cikinsu Yana Qoqarin Riqe Wani Aiki Guda ‘Daya Da Zai Iya Zamto Masa Sanadin Tsira a Nan Duniya (Mai Gushewa) Da Kuma Lahira.

Ban Tsammanin za ka iya riƙe hawayenka idan Ka Karanta irin ibada tare da ƙoƙarin Sirranta da Suke, Za ka Yarda Mukam Sai dai Allah Ya Jiƙanmu.

A Cikinsu ne fa Za Ka ji Wani; Ya Shekara 40 Bai Taɓa rasa Kabbarar Harama Ba. Yayi Saukar Al-Qur’ani Sau Dubu 24. Ya Shekara 40 Yana Azumi, Matarsa Ma ba ta Sani ba. Ya yi Tsayuwar dare a duhun Saman Gidansa. Ya ɗauki nauyin marayu, Sai bayan Ya Mutu a gane. Ya yi Kuka har idanunsa Sun Gaza Hawaye.

Akwai Wani Sirri Da Sirri Tsakanin Ka Da Allah…?

Nemo Amsar Tambayar Yanzu Ba Sai Anjima, Wanne Aiki Guda ɗaya Tak Ka Taɓayi, Wanda Babu Wanda Ya Sani, Baka Faɗawa Kowa ba, baka nunawa Kowa ba, daga Kai Sai Mahaliccinka a ɓoye, Ka Tuna…???

Azumi ne a ɓoye?Karatun Qur’an Ko Zikiri ne?Kuka ne  Cikin daren da babu Mai Jinka?Sadaƙa Ce da Wanda Ka yi wa bai Sanka ba?Ko Sallah ce Raka’a Biyu tuna dai.!!! Babu.

Ko Saɓonsane Kawai Ke Haɗaku a Sirri…!!!Yi ƙoƙarin Samar Da ɗaya, Zaɓi Ibáda Da Allah (T) Yafi So, Ka yi ta Ba Tare Da Sanin Kowa ba, Ka Kyautata niyyarka, Bayan Ka gama Ka Godewa Allah (T), Ka Yabe shi da yabon da baka taɓa Masa irinsa ba, Ka yi wa Annabinsa Salati, Sannan Ka ce Ya Allah , Wannan Ibadar dana yi Sirri ce Tsakanin Ni Da Kai.

Mayar Da Hakan ɗabi’arka, Kajira Kaga Sakayyarsa.!!!Daga wani Dan uwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *