Tsohon shugaban karamar hukuma ya yi shagube kan bashin biliyan 65.7 da gwamnatin Tambuwal za ta ci a Sokoto

Tsohon shugaban karamar hukumar mulkin Sokoto ta Arewa Alhaji Abdullahi Hassan daya daga cikin jigogin jam’iyar APC a Sokoto ya yi fice a wurin son aiwatar da aiyukkan cigaba a jihar.

Tsohon shugaban ya daina magana a kafafen yada labarai kan yadda gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ke tafiya kamar yadda aka saba jinsa a farkon wa’adin mulkin Tambuwal, har yanzu bai bayyana dalilinsa na kama bakinsa ba, duk da yanzu ana ganinsa yana yin shagube a turakarsa ta facebook lokaci-lokaci.

Managarciya ta samu wani shagube da tsohon ciyaman din ya yi in da yake cewa ‘Duk wanda ya aje naira biliyan 65.7 a zaben 2023 sai an yi daga da shi’

Wannan shaguben nasa karara yana nufin bashin da Gwamnatin Tambuwal za ta ci ne yake magana, yana nuna kudin ba aiki za a yi da su ba ajiyewa za a yi domin tunkarar zaben 2023.

Abdullahi Hassan ya kara da cewar shi baya kara fitowa takara sai an bar sayen kuri’a don ba zai yarda ya kashe abin da yake da shi ba, masu ruwa da zaben da aka yi takara da shi su rubuta wanda suka ga dama, ba wanda ya ci zabe ba, tun da ba su tsoron Allah.

Ya juya kan masu mulki ya ce “Ku yi ta sata babu aiki, Allah nada hanyoyin kama ku” a cewarsa.

Ya ce wadan nan kalaman da yake yi ba hasada ce yake yi ba yana yi ne domin halin da na bayansu za ta shiga, shi yana da harkokinsa na kasuwanci da yake yi ba ruwansa da jiran gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *