Spread the love

Shirin da gwamnatin tarayya ke yi na mika Dalar Amerika miliyan 100 a cikin kudin Abacha da aka karbo, da za a hannunta kudin ga Gwamnan Kebbi Sanata Atiku Bagudu jigo ne a jam’iyar APC ya haddasa cece-ku-ce da baiyana bacin rai a tsakanin mutanen Nijeriya.

Gwamnatin Buhari ta ce yarjejeniyar da aka yi shekara 17 tsakanin gwamnati da Bagudu ne ya sanya za a bashi kudin kan taimakon Nijeriya da ya yi kan lamarin da ya faru a karamar kotu a Washington.

Gwamna Bagudu ya karyarta ya aikata wani abu da ba ya da kyau kuma yarjejeniyar an yi ta ne tun lokacin mulkin Obasanjo.

Mutanen Nijeriya suna ganin ba wannan lokacin ne yakamata a baiwa Bagudu kudin ba ko da an yi bincike sosai an tabbatar bai aikata wani abu da baya da kyau a wurin kai kudin ba, kuma ya taimaki Nijeriya wurin dawowar kudin, tau ya dace a dubi halin da kasar ke ciki na matsin tattalin arziki da rashin wadatattun kayan more rayuwa a sanya kudin a can kafin daga baya a waiwayo yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *