Spread the love

Babu ƙasar da za ta iya samarwa matasanta aiki gaba ɗaya dole ne mu yi tunani fiye da abin da muke da shi, halin da Nijeriya take ciki a yau an fita batun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da suka iya taka leda ga shi kuma duniya nemansu ta kowace hanya domin su tafi su buga masu ƙwallo anan ko a waje, hakan ya sanya muka samar da tsari da zai sanya matashi mai sha’awar wasan ƙwallon ƙafa ya koyi wasan ƙwallon da karatu lokaci ɗaya ba tare da ya rasa kowane ba.

Shugaban cibiyar bunƙasa wasanni ta Afirika(President African Sport Development Centre) Honarabul Faruku Malami Yabo ne ya sanar da haka a wajen bukin yaye wasu matasa da suka samu horaswa ƙarƙashin cibiyar a Abuja.

Ya ce sun fito da tsarin ne domin suna son matasan ‘yan ƙwallo da ke tasowa su samu zaɓi biyu kana iya aiki da karatun da ka kammala ko da ka samu cikas a wajen wasanka, abin da ba a fata.

Ya ce sun fahimci an bar abu mai muhimmanci a Nijeriya a Turai ma suna sanya wasan ƙwallo a cikin tsarin ilminsu. Alƙalin wasa da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa karatunsu ake yi, sai mai ilmin fannin ne zai yi.

Faruku Yabo ya ce alherin da ƙasar Argentina da Spain da Brazil suke da shi bai fi wasan ƙwallon ƙafa ba ya taimaki tattalin arziki da martabarsu. Nijeriya ma ya kamata ta bunƙasa haujin.

Da farko Yariman Yabo ya godewa jagoran ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya(Super Eagle) Ahmad Musa kan gudunmuwar da ya baiwa matasan na ƙarfafa su sosai, ya yi masa godiya ta musamman ganin komai tare da shi aka yi a bukin yaye ɗalibban.

Ya ce wannan ƙudiri sun fara shi ne shi da mataimakin Gwamnan Kano tun a shekarar 1999 da zimmar taimkawa matasa a ƙarfafe su ga abin da suke sha’awa, an yi nasara domin an samu sakamako mai kyau da sauri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *