Buhari ya ba da sharaɗin buɗe iyakokin Nijeriya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ba da sharadin bude iyakokin kasar Nijeriya don barin kaya su shigo daga kasashe masu makwabtaka.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a lokacin da ya hadu da Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore wanda ya kai masa ziyara a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Abuja, kamar yadda Channels TV suka ruwaito.

A yayin ziyarat Buhari ya fada masa cewa “Babbar matsalarmu shi ne tsaro, shigo da makamai, harsasai da kuma kwayoyi,”.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara da cewa, “mun fahimci raguwa a ta’addanci tun bayan da muka rufe iyakokin kasarmu. Hakazalika, manonanmu yanzu na iya siyar da shinkafar gida tunda mun dena shigo da ta Turai wacce ke cika kasar nan.”

Ya sanar da bakon nasa cewa Najeriya ta yanke hukuncin sakaya iyakokinta ne saboda tabbatar da tsaron kasa .

Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar yace bude iyakokin kasar ya dogara ne a kan rahoton kwamitin bangare uku da ya hada da gwamnatocin Najeriya, jamhuriyar Benin da jamhuriyar Nijar Yace za’a bude in komai ya daidaita.

Yace “Zan yi aiki da gaggawa matukar na samu rahoto,” – inji Shugaba Buhari.

Daga karshe dai Shugaban Burkina Faso ya nemi Shugaba Buhari da ya kara duba matsayarsa.

Maganar buɗe iyakokin Nijeriya an yi ta yinta amma abin da ya canja duk da an yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta duba halin da talakawa suke ciki musamman waɗan da ke kusa da iyakokin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *