Spread the love

‘Yan sandan jihar Sokoto sun kama Darakta da wasu mutum biyu ma’aikatan hukumar tsaftace birnin Sokoto kan zargin sun yi wa yarinya mai sayar da ruwan leda ‘yar shekara 14 ciki, da kuma barazanar da suke yi wa Antinta.

Wadan da ake zargin sun hada da Daraktan Kudi na hukumar Ahmad Yahaya Nawawi da maibincike(internal Auditor) Ibrahim Isa da wani Habibu Abubakar

Haka kuma sun kama Kodinetan Freedom for Humanity, Kwamred Hussaini kan zargin ya amshi kudi ga wanda ake zargi domin ya yi shige da fice ya tabbatar maganar ta mutu a wurin hukumar NAPTIP. 

Manema labarai sun ga mota Marsidis da aka karbo wajen dan rajin kare dan adam din.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ASP Sadik ya tabbatar da kamen ya ce za su kira taron manema labarai bayan sun kammala bincike.

Kwamandan yanki na hukumar NAPTIP, Abubakar Abra ya tabbatar da ya karbi takarda daga hidikwatarsu ta neman ya mayar da lamarin gare su domin domin abun ya shafi ƙaramar yarinya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *