Spread the love

 Babbar kotu dake jihar Kano  ta yanke hukuncin kisa ga matar da ta jefo mijinta daga saman bene waton gidan sama abin da ya zama silar ajalinsa.

A ranar Juma’a ne kotun ta yanke hukuncin wanda  Alkhali  A. T Badamasi, ya jagoranta.

Rashida Sa’idu mai shekaru 31 ce ta aikata laifin, sakamakon haka aka yanke mata hukuncin kisa, bisa zargin kashe mijita Adamu Ali ta hanyar turo shi daga saman bene, laifin da ta yarda ta aikata.

Rashida dai ta aikata laifin a ranar 20 ga watan fabrairun 2019, a unguwar Dorayi dake birnin Kano, ta yi hakan ne  bayan rikicin da ya shiga tsakaninta da shi. Rashin fahimtar  ya barke tsakaninsu ne bayan da ta ji shi yana waya da wata mace da take zargi budurwarsa ce.

Bayan ta turo shi daga benen ne,  ya fado ya karye a wuya, hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Rahotanni dai sun bayyana cewar Rashida na da ‘ya’ya biyu, da mai gidan nata, sannan ita ce matarsa ta biyu a lokacin da abin ya faru.

 Kafin auren nasu, sun hadu da mijin nata ne a makarantar kwalejin fasaha ta tarayya dake Kano, ita dalibar Adamu Ali ce, a inda bayan daukar wani lokaci suna soyayya har suka kai ga yin aure kamar yadda Managarciya ta samu labari.

Kafin Rashida ta aikata laifin  sai da ta fara kai wa kishiyarta korafi, in da ta sanar da ita cewa, ta ji mijinsu yana waya da wata  budurwarsa,  abokiyar zaman nata ta ba ta shawarar barinsa ya ci gaba da wayar, amma ta ki, a cewar wata majiyar.

 Rashida na da damar daukaka kara zuwa kotun daukaka kara dake Kano, nan da wata uku idan har bata gamsu da hukuncin da babbar kotun ta yi mata ba, kamar yadda manema labarai suka ruwaito.

An dai fara sauraren shari’ar ne tun a ranar 31 ga watan Mayu 2019, sai a wannan Jumu’ar ta zo karshe.

Wannan halin bakin kishi da matan wannan zamani suka sa a zuciyarsu yana wahalar da su da sanya su shiga halin dana sani, yakamata su yi wa kansu karatun ta natsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *