Gwamna Tambuwal ya kaddamar da rabon bashin biliyan 1 wanda babu ruwa a cikinsa

Gwaman jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon bashin biliyan daya ga kananan ‘yan kasuwa wanda babu ruwa cikinsa, a lokacin bukin bude bankin  Giginya Microfinance mallakar gwamnatin jihar Sokoto.

Bashin wanda za a biya cikin shekara biyu ana saran kusan mutum 5000 ne za su amfana da bashin kuma kashi 30 na mutanen mata ne kamar yadda gwamna ya bukaci a yi hakan.

Mutanen da za su amfana an zabo su ne a dukkan mazabun jihar Sokoto a kananan hukumomi 23, kowace mazaba an dauko mutum hudu, na daya zai kabi bashin miliyan daya na biyu dubu 500 na uku dubu 200 sai na karshe dubu 100, a kowane wata akwai abin da mutum zai biya har ya kammala biyan kudin cikin shekara biyu.

Gwamnan a cikin jawabinsa ya gargadi ‘yan siyasa da kar su sanya kansu cikin wannan lamarin domin ba kudin siyasa ba ne kudi ne na ‘yan kasuwa domin a tallafa masu ga jarin da suke da shi.

Haka kuma ya yi kira ga daraktocin Bankin su sanya kwarewarsu wurin ganin bankin ya tsayu da kafafunsa domin cigaban jihar Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *