Spread the love

Mai martaba Sarkin Kano  Muhammadu Sunusi na II ya yi kira ga daukar mataki a jihohi ga masu wasa da hakkin aure, yakamata a kama duk wani uba mai wasa da nauyin da Allah ya daura masa har yake tura ‘ya’yansa wurin Almajirci don su tafi suna yin baran abin da za su ci.

Sarki ya fadi haka taron da gidauniyar Uwar shugaban kasa Aisha Buhari, (Future Assured)  tare da hadin gwiwar Majalisar harkokin addinin Musulunci ta kasa suka shirya a ranar Alhamis data gabata ya ce  duk Uba da ya tura dan sa almajiranci da a kama shi. Sannan ya yi kira ga Gwamnoni da ‘yan majalisu da su samar da irin wannan doka.

Sarkin ya bayyana cewa babu dokar da ta ce mutum ya yi aure ya hayayyafa kuma ya kyale ‘ya’yan sa tare da daukar dawainiyar su ba. Sannan ya ce duk magidancin da yake ganin bai da karfin daukar dawainiyan iyalin sa da ya fita bara da kansa ba ya tura ‘ya’yan ba.

Ya kara jaddada cewa yana kan bakarsa ko shekara 100 za a yi na cewa ba daidai ba ne kuma ba koyarwar addinin musulunci ba ne magidanci ya bugi matarsa, yakamata gwamnoni da majalisun jihohi su yi doka kan wannan domin kwatarwa mata ‘yancinsu.

Ya kuma bayyana cewa ya fi dacewa idan namiji ya saki matarsa da ya tattara na shi ya na shi ya koma gidan iyayensa ya bar mata gidan da yaranta maimakon ya tura ta gidan iyayenta da tarin yara.

Ya kuma kara da cewar bai kamata don mutum ya saki matsarsa bay a bar ciyar da yara hannunta da kulawa da su hakan ke sa ana samu ‘yan bangar siyasa a cikinal’umma, hargitsi na yawaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *