Spread the love

Jarumi a masana’antar shirya finafinnan Hausa Sadik Sani Sadik ya ce baya da budurwa a masana’antar shirya finafinnan Hausa matarsa dake gida ita ce budurwarsa, amma yana da Aminiya a Kannywood waton Rahama Sadau.

“Nafi yarda da ita fiye da kowa, nasan za ta rufe min sirrina yanda zan rufe nata muna da kyakkyawar alaka a tsakaninmu”

Jarumin ya furta hakan ne a wata fira da gidan rediyon BBC ya yi da shi ya ce shi ba ya da uban gida a Kannywood don ba wanda ya koya masa sana’ar da yake yi amma akwai mutanen da yake girmamawa saboda wasu dalilai.

“Bello Muhammad Bello(BMB) ta dalilinsa na shigo harkar fim, sai Ali Nuhu na zauna gidansa a lokacin da na zo Kano, Malam Aminu Saira a lokacin da duniya ba ta yarda zan iya ba shi ya yarda zan iya ya rika sanya ni manyan finafinnansa ciki har da Dan Marayan Zaki, wannan dalilin nake ganin kimarsa.”

“Akwai Umar UK ya yi min fim masu girma, akwai Adam A. Zango na zauna karkashin kamfaninsa, ina girmama wadan nan mutane amma bani da ubangida a Kannywood”. a cewarsa.

Managarciya ta fahimci masana’antar shirya finafinnan Hausa na cike da butulci, duba da wadannan kalaman na wannnan jarumi da ya ka sa daukar dayan cikin ukun nan matsayin ubangidansa, waton wanda ya yi silar shigarsa harkar fim ko wanda ya zauna gidansa ko wanda ya zauna karkashin kamfaninsa, duk wadan nan a ce ba su taka rawa a rayuwarsa da za ta zama ta tsakanin yaro da ubangida ba?.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *