Spread the love

Gwamnatin Nijeriya ta ce ba za ta cigaba da sanya tallafi ga haujin wutar lantarki ba.

Ta yi kira ga kamfanonin rarraba wutar lantarki su ba da hanya ga masu zuba jari in ba za su iya abin da ya dace su yi ba, a wannan lokacin da ake sanya tallafi ga haujin.

A watan da ya gabata majalisar tattalin arziki na kasa ta ce gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kashe Tiriliyan 1.7 ga haujin a cikin shekaru uku da suka wuce.

A bayanin da yake yi wa manema labarai ministan wutar lantarki Sale Mamman bayan kammala zaman majalisar zartarwar kasa ya ce gwamnati ba za ta cigaba da sanya tallafi ba, saboda kamfanonin suna karbar wuta Megawatts 3000, amma suna biyan ta Magawatts 1000 daya ne kawai, kashi 15 na abin da suke karba kenan. Gwamanti ke cika sauran kudin Megawatts.

“Ba za mu iya cigaba da hakan ba, in sun shirya cigaba da hakan ya yi amma dai mu ba za mu cigaba ba, za su iya bayar da hanya ga wadan da suka shirya su zo su zuba jari, sai mu roki gwamnati ta duba in za su iya shi kenen. Amma in ba za su iya ba sai su ba da wuri.” a cewarsa.

Ya ce gwamnati ta sanya hannu a takardar yarjejeniya da gwamnatin Jamani kan abubuwan wutar lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *