Spread the love

Gwamnatin jihar Kebbi za ta kashe miliyan 650 a bukin kamun kifi da al’adu na kasa da kasa da za a gudanar a karamar hukumar Argungu a watan Maris na shekarar 2020.

Kwamishinan aiyukka Abubakar Chika Ladan bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar ya fadi hakan ya ce Sama da miliyan 650 ne aka ware domin gudanar da bukin kamun kifi da al’adu wanda za a yi watan Maris.

Ya ce kudin za a gyara gine-ginen da suka lalace a wurin da hanyoyi da rumfar manyan baki da wurin kamun kifin da Otal da sauransu, an riga an fara gudanar da gyare-gyaren za a kammala aikin a lokacin da aka ba su.

Chika Ladan ya tunatar da cewa babban kwamitin shirye-shirye an kaddamar da shi karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jiha Samaila Yombe.

Ya ce kwamitin ya fara tsare-tsarensa tare da karamin kwamitin masarautar Argungu akwai kananan kwamitoci sama da 20 da aka daurawa alhakin duba kowane bangare na bukin domin samun nasara.

‘Suna aiki tukuru domin su kammala a daidai lokacin da aka ba su, mun gamsu tsare-tsarensu da tunaninsu gaba daya za su kammala bukatar mu a karshen wannan watan’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *