Spread the love

Tare da Malam Sharif Usman Baban Umma

Zagin Shariffan Sokoto ta kudu

“YA’AYU HANNASUT TAQU RABBAKUMUL LAZI HALAQAKUM MIN NAFSIN WAHIDA WAHALAQA MINHA ZAUJIHA WABASSA MIN HUMA RIJALAN KASIRA WANISA’A”

Ma’ana

Allah mai girma da daukaka Ya ce ya ku mutane ku ji tsoron Allah, wanda Ya halicce ku daga rayuwa daya, kuma Ya halitta daga gare Shi ma’aurata daga ciki Ya watsa daga gare su maza da Yawa da Mata.

Bayan Haka Allah mai girma da daukaka Ya girmama Mata Kuma Ya ba su Matsayin da babu Wani Addini da Ya ba su kwatan kwacin na musulunci.

01. Macce ce ta Samu Darajar Zama ta 2 a halittar Dan Adam bayan halittar Annabi Adam A.S Sai Allah Ya Halitta Sayyida Hauwa’u daga kashin Awazar(hakarkarin) hagu ta Annabi Adam A.S,

02. Mace ce Allah Ya Jibinta lamarinta da Sha’aninta ga Namiji Don girmamawar da Allah Yayi mata a cikin al’umma,

03. Mace ce Allah ya ba ta karuwar al’ummar a hannunta ta hanyar ba ta amanar renon Dan’Adam a cikinta, tun yana Maniyi har zuwa haife shi, shayar da shi da kuma renon tarbiyar sa,

04. Mace ce Allah Ya ba ta matsayi a Alqur’ani in da ya sanyawa sura sukutum Sunan Mata ita ce ‘Suratun Nisa’i’,

05. Mace ce ta fara Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa, kuma ake koyi da ita har karshen Duniya, Sayyida Hajaru A.S,

06. Mace ce Sanadin Musuluntar Sayyadina Umar A.S waton Nana Fadima A.S,

07. Mace ce take Samun ladar Jam’in Salloli biyar da Salar Jum’a da Salar Jana’iza da ladar masu fita Jihadi, matukar ta bi mijinta ta yi masa biyayya,

08. Mace ce ta kwantarwa Annabi Muhammadu (S.A.W) hankali lokacin Saukar Wahayi ta ce Allah ba zai bari wani mumunan lamari ya faru da kai ba, Sayyida Khadijat A.S,

09. Mace ce sanadin samun Taimama a Musulunci Sayyida Nana Aisha A.S,

10. Mace ce sanadin tsirar Sahabbai daga fuskantar fushin Allah lokacin da an ka yi sulhun Hudaibiya Nana Ummu Salma A.S,

Nan Zan dakata Sai mun hadu a Darajojin Mata Kashi na 2 Allah Ya yi mana Jagora, Allahumma Sali wa Sallim ala Hairil halqillah nabiyi Rahamatu Annabi Muhammadu ( S.A.W ) Allahumma la’ilma Lana ila ma Allamtana inaka antal Alimul Hakim.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *