Spread the love

Jagoran Kwankwasiya na Najeriya kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya buƙaci a sake bitar hukuncin Kotun ƙolin Najeriya akan shari’ar Gwamnan Jihar Kano.

Wannan yana kunshe ne a cikin takar da Ibrahim Abba, mai taimakawa ɗan takarar gwamnan jahar Kano na PDP, akan yada labarai Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu.

Ya ce kwankwaso ya furta haka a lokacin da ya kai ziyara ga shugabanin zartawa na jam’iyar PDP ta kasa.

Kotun ƙolin Najeriya dai ta yi watsi da shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya saka a gabanta yana ƙalubalantar nasarar Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje, in da Ganduje ya samu zama zakara a zaben gwamnan da ya gabata a shekarar 2019.

Kano ta zama jiha ta huɗu da ke buƙatar kotu ta yi bitar hukuncin da ta yi a farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *