Spread the love

Daliban Sikandare a jihar Sokoto dake shekarar karshe su dubu bakwai da dari biyu da ashirin da uku(7,223) ne ba su cancanci gwamnatin jihar Sokoto ta biya musu kudin rubuta jarabawar kammala siandare ba waton WAEC da NECO.

Daraktan kula da jarabawa a ma’aikatar ilmin Furamare da Sikandare ta jihar Sokoto Malam Shehu Muhammad Lema ne ya sanar da hakan a lokacin da yake magana kan sakamakon jarabawar gwaji(MOCK) da aka fitar wanda ma’aikatar ta gudanar a kwanakin baya.

A bayanin da ya fitar wanda jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Nura Bello Mai kwanci ya sanyawa hannu ya ce daliban sun kasa samun nasarar da aka shardanta.

Malam Lema ya ce dalibai dubu 25 da 393 ne za su zauna jarabawar, amma dalibai dubu 18,170 suka cika sharuddan da ake bukata.

A cewarsa shurddan da ake bukata dole ne dalibi ya samu nasarar a darasi uku daga cikin biyar da aka yi jarabawa kansu.

Gwamnatin jihar Sokoto ba ta kyautawa dalibban ganin yanda aka yi masu jarabawar shiga ajin karshe waton SS3 kuma ma’aikatar ta shirrya jarabawar suka samu nasara, lokacin shirya jarabawar ta gwaji(MOCK) wasu na ganin ba a baiwa dalibban damar karatu ba, kafin haka an yi wa dalibban tantancewa ta samu gurbin rubuta jarabawar yanzu kawai a dakatar da su abin da wasu ke ganin yana iya barin baya da kura bayan tabarbarewar karatu da za a samu a jihar Sakkwato.

Wani malami da ya yi magana da manema labarai ya ce “Darasi biyar ne aka rubuta jarabawarsu Physics da Chemistry da English da Mathemathics da Biology cikin darasi 9 da ake zana jarabawar ƙarshe ta sikandare, dukkan wadan nan darussan biyar suna da karancin malamai a makaratun sikandaren jihar, akwai makarantar da za ka samu ba malami gaba daya a dayan darussan nan da aka yi jarabawa kansu, ta yaya yaro zai samu nasara ga abin da ba a koyar da shi ba.” a cewarsa.

Ya ce an kammala yi wa yaran rijista a makarantunsu sauran kawai a yi masu na jarabawar da za su rubuta ga shi an fito da wannan maganar, na ba gwamnati shawara kar ta tsaya kan wannan hukuncin domin rashin adalci ne ga yaran wanda zai iya haifar da matsala a jihar nan.

“Ranar 21 ga wannan watan ne za a rufe rijistar WAEC jumu’a kenan kuma anan Sokoto ba a fara rijistar ba ga wannan abu an fito da shi, yakamata ma’aikatar ilmi ta zauna ta duba lamarin mafiyawan yaran da aka ce ba su yi nasara ba ‘ya’yan talakawa ne uwayensu ba su iya fittar da dubu 13, 950 su yi masu rijistar WAEC, kuma su sake fitar da wasu dubu 11000 su saya masu NECO, makomar yaran tana da matsala kuma bai kamata gwamnati ta yi wasa da wannan ba.” a cewarsa.

Ya ce kar amanta da abin da ya faru a Sikandaren Sani Digyadi da aka yi wa wasu yara Repeat suka kone block din makarantar gaba daya domin an fusata su.

Jihar Neja da Kebbi suna yin MOCK a matsayin jarabawar shiga ajin ƙarshe in ka samu nasara shikenan za a biya maka jarabawar daga gwamnati, akwai buƙatar sake duba lamarin nan na Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *