Spread the love

Kasuwar masu gyaran wayar hannu da sayarwa a birnin Maiduguri jihar Borno an rushe ta domin rashin hanyar da jami’an tsaro za su bi su kai ga shagunan dake wurin.

Babbar motar da ke rushe gini ce ta zo a wurin ta sauya wa gaban kasuwar fuska, yayin da wasu motocin sintiri na ‘yan sanda ke jibge a wasu wuraren kasuwar na musamman don jiran ko ta kwana.

Matasan da ke wurin suna kallon yanda lamarin ke tafiya a fuskokinsu ba farinciki suna gefe sun dan yi nisa in da aike aiwatar da lamarin, suna bakin kasuwar Jagwal.

Da yawan kananan ‘yan kasuwar da aka yi fira da su ba su san dalilin rufe shagunansu da aka yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *