Sarkin Kano ya ce Arewa ita ta rushe kanta da kanata


Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi wannan maganar ne a jiya Litinin a gidan gwamnatin jihar Kaduna yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Nasir El-Rufai  shekara 60 da haihuwa. 


Sanusi ya ce a matsayin shugaba, ya maimaita abinda ya  tarar ana yi tare da tsammanin za ya banbanta ba dai-dai ba ne. Ya kara da cewa, canji zai samu ne a Arewa idan aka fara yin abubuwa mabanbanta.


 Ya jinjinawa salon gyaran bangaren ilimi na gwamna El- rufai. Ya ce hakan ne kawai zai iya tseratar da Arewa. 


“Dai-dai ne idan gwamna ya bi salon da ya tarar na mulki a cewar mutanen Arewa. Amma ba dai-dai ba ne gaskiya idan ya bi salon da bai kawo wani canji ga yankin.


 Idan kuwa shugaba ko mai mulki yayi hakan, zamu iya cewa yana daga cikin matsalar yankin nan,” Sanusi ya ce.


 “Babban canji a Arewa zai zo ne bayan mun gano cewa sai mun banbanta da sauran. Idan arewa ba ta canza ba, za ta halaka kuwa. Idan bamu canza ba, akwai lokacin da mun sani da zai zo.” in ji shi.


 “Sauran yankuna a kasar nan na zuba kudi wajen ilimantar da yaransu tare da yaye dalibai daga manyan makarantu amma mu ba mu yin haka. 
Wadannan yankunan ba zasu zuba ido su kasa hayewa shugabancinmu ba saboda ba daga yankin da ya kamata suke ba, bayan mun gaza gina ‘ya’yanmu.” cewar Sarkin. Ya bayyana cewa, babu wani shugaba a Arewa da zai samu farin ciki bayan yana zagaye da matsaloli a yankin.Saura da mi Sarkin Kano ya yi nasa abin da yakamata ya yi don haka shugabanni su tashi tsaye wajen kawo gyara kafin kowa ya durmuya. 


“Babu wani shugaba a Arewa da zai ce yau yana cikin farin ciki,” Sanusi ya ce.


 “Ba za ka zama cikin farin ciki a Arewa ba bayan kashi 87 na talaucin Nijeriya na Arewa. Ba yadda za a yi ka yi farin ciki bayan yara da yawa ba su zuwa makaranta a yankin nan.


 Ba yadda za a yi ka yi farin ciki bayan akwai matsalar Boko Haram.”

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *