Spread the love

A litinin data gabata Haruna Yusuf (Baban Chinedu) ya fitar da bidiyo a shafinsa na Facebook yake bayyana cewa Malam Ismael Na’abba Afakallah ya cinye kudade har naira Miliyan Biyar da Gwamna Ganduje ya bayar domin ayiwa yarinya ‘yar gidan Marigayi Rabilu Musa (Dan Ibro) don hidimar buki.

Baban Chinedu ya nemi al’umma da su taimaka su shiga cikin lamarin domin a kwatowa iyalan Ibro hakkinsu, sannan ya nemi da malamai da suma su shigo domin nemawa marayu hakkinsu da Afakallah ya cinye.

Malam Ismael Afakallah bai san da wannan maganar ba, Babu inda Gwamna Ganduje ya bashi kudi, babu wani mutum daya bashi kudi don ya kaiwa iyalan Ibro da har zai cinye.

Afakallah ya umarci lauyoyinsa da su shigo cikin lamarin bata masa suna da Baban Chinedu ya yi.

Lauya Abdullahi Musa Karaye tare da abokan aikinsa lauyoyin dake kare Malam Afakallah, sun umarci Baban Chinedu ya sauke bidiyon daya saka a dukkan shafukansa sannan ya sake yin wani bidiyon na bayar da hakuri tare da karyata kansa, idan wa’adin ya cika ba tare da yayi hakan ba, za su garzaya zuwa kotu domin nemawa Malam Afakallah hakkinsa akan wannan bata sunan da akayi ma.

Cikin awa ishirin da hudu kacal ake bukatar ya cire Bidiyon kuma yayi sabo na bayar da hakuri, idan ya gaza yin hakan,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *