Spread the love

Hajiya Maryam Yusuf  ‘yar uwar mahaifiyar yarinya ta zargi an baiwa mahaifin yarinyar dubu 250 don ya rufe maganar kar ta fita, har ya yi amfani da wani kaso na kudin ya sayi fili.

Malam Muhammadu maifin yarinyar ya ƙaryata zargin. Ya ce ya karɓi dubu 50 ne kadai ga wanda ake zargin ya yi wa ‘yarsa ciki, a lokacin da baya da lafiya.

Ya ce ya janye maganar ne aka yi sulhu domin mutunci da yarda da ƙaddara domin shi musulmi ne.

Kodinetan hukumar kiyaye haƙƙin Ɗan’adam a Sokoto Barista Hamza Liman ya ce yana sane da lamarin kuma za su bi har karshen lamarin sai sun tabbatar da an yi adalci.   

Daraktan Kudi Ahmad Yahaya Nawawi da wani Habibu Abubakar dukkansu ma’aikata ne a  hukumar kula da tsaftar birnin Sokoto su ne ake  zargi da yi wa  karamar yarinya ‘yar shekara 14 ciki a lokacin da take sana’arta ta tallar ruwan leda.

An zarge su da saduwa da ita a ɗaya daga cikin ofisoshinsu abin da ya kai ga shigar juna biyu yanzu wata shida da samun cikin.

Waɗanda ake zargin sun aminta da sun aikata laifin a bayanan da suka yi daban-daban a ofishin yanki na hukumar kula da safarar yara ta kasa(NAPTIP). Amma daga baya sun ce ƙage ne aka yi masu.

labari ne da jaridar dailƴ trust ta wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *