Spread the love

A kalla mutum 22 ne ‘yan rakiyar amarya zuwa gidan mijinta suka rasu a hatsarin mota da ya faru a ranar Assabar da ta gabata kan hanyar Kankiya zuwa Danja a jihar Katsina.

Mutum goma 17 ne suka samu munanan raunuka yayinda amarya ta tsallake rijiya da baya.

Hatsarin ya auku bayan batagari sun kashe mutum 30 a cikin al’ummar tsauwa-Dankar a karamar hukumar Batsari jihar ta Katsina.

Hadarin ya faru kunsan garin Kafur mota bus kirar J5 da wata motocin biyu bayan su sha juna mutum 22 ya kone abin da ya yi sandin mutuwarsu.

Wani da lamarin ya faru gaban idonsa ya ce mafiyawan wadanda ke cikin hatsarin yara ne da mata ‘yan rakiyar amarya.

A cewarsa Amarya da dayan direba da wani su uku ne suka tsira.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar kiyaye haddurra ta jihar Katsina Abubakar Usman ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutum 11 ne suka samu rauni an kai su babbar asibitin Malumfashi, wadanda suka kone ba a ma iya gane su an yi masu sutura kamar yadda musulunci ya tanadar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *