Spread the love

Shugaban kungiyar Gwmnonin jam’iyar  PDP, Gwamnan  jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a yau tare da takwarorinsa biyu a jihohin  Adamawa,  Bauchi da wasu shugabannin  PDP suna a Port Harcourt, gidan gwamnatin jihar Rivers a yunkurinsu na magance rikicin da jam’iyarsu ke fama da shi.

In ba a manta ba a kokarin samar da zaman lafiya a cikin jam’iyar PDP shugaban jam’iyar na kasa da Gwamna Tambuwal sun yi ta zama da bangarorin da ke rikici domin dai a dunke baraka a yi tafiya tare cikin hadin kai saboda jam’iya ta kara samu cigaba.

Shuaban amintattaun jam’iya Sanata Walid Jibril yana cikin shirin dunke barakar da ke tsakanin Dickson da Wike.

Tambuwal bayan shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin PDP ana zaton zai yi takarar shugaban kasa a jam’iyarsu ganin yanda ya nema a farkon wa’adin mulkinsa na farko, balle yanzu da zai kammala wa’adi na biyu, ana danganta yunkurin sasancinsa da son cimma burinsa bayan na jam’iya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *