Spread the love

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Janar Babagana Monguno, ya zargi Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da yi wa harkokin tsaron kasa katsalandan da saka baki a abubuwan da ba shi da iko akai.

A dalilin haka Mongonu ya aika wa manyan hafsoshin Najeriya dake shugabantan rundunonin tsaro na sojoji da wasikar gargadi cewa kada su kuskura su rika karbar umarni daga Abba Kyari daga yanzu.

A wasikar da majiyar mu ta PREMIUM TIMES ta gano, Monguno ya ce a lokuta da dama Kyari ne ya ke yin gaban kansa yake ba manyan hafsoshin rundunar sojoji umarni ba tare da Shugaban Kasa Buhari ya sani ba, kuma hakan ya na kawo wa harkokin tsaro cikas matuka.

“Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba ya cikin jerin masu iya zartar da wata doka a kasar nan sannan bai yi rantsuwa don kare kasa Najeriya ba saboda haka babu dalilin da zai sa ya rika cusa baki a harkokin kasa ba.” Inji Janar Monguno.

“A dalilin haka bai kamata ba saɓawa doka ce ya rika ganawa da ta musamman da manyan hafsoshin Najeriya da shugabannin tsaron kasa da jakadun ƙasashen waje ba tare da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ministocin da ya kamata su na tare a zaman ba. Yin haka saba wa dokar kasa ce.

Ya ce Ire-iren wadannan zumudi, da cusa kansa a binda ba huruminsa ba ne da nuna isa da ba da umarni ba tare da Buhari ya sani ba da Kyari ya ke yi, suna kawo mana cikas a ayyukan samar da tsaro a kasa Najeriya da kuma koma baya da ake samu wajen tabbatar da samun nasara a ayyukan da shugaba Buhari ya sa a gaba.

Wannan wasika na Monguno ta zo ne a daidai matsalar tsaro ta dawo ɗanye a ƙasar nan sanan ‘yan Najeriya na kuka akai matuka.

Idan dai ba a manta ba matsalar tsaro ya na neman ya gagagri jami’an tsaron kasar nan a ‘yan kwanakin nan, harkar satar mutane da yawan ta’addanci suna ƙaruwa a jihohin Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *