Spread the love

   

Tun bayan hukucin kotu koli kan zaben Gwamna jihar Bayalsa a 2019 an cigaba da musayar kalamai a tsakanin jagororin jam’iyar a fadin Nijeriya tare da kira ga wadanda suke kanwa uwar gamin lamarin su ja baya ga harkar jam’iya abaiwa wadanda ke iya kai jam’iyar tudun mun tsira.

A musayar yawun mambobin jam’iya sun ta’alaka faduwar ga sakarcin jagororinsu musamman sakakacin shugaban jam’iyar na kasa Adams Oshiomhole.

Karamin ministan Kwadago Festus Keyamo ya daura laifi ga shugabannin jam’iya da suka kasa yin tantancewa mai kyau a cikin gida.

Ya ce aikin da kotun koli ta yi kan zaben fitar da gwani abun yabawa ne, a gefen jam’iya a zo a gyara abubuwa gudun kar a sake samun wannan cikas a gaba.

Jigo a jam’iyar APC a jihar Edo Charles Idahosa ya soki yanda shugabansu ke tafiyar da jam’iyar, cikas da yake kawo mata yafi cigabanta, rashi iya jagorancinsa ne ya sa suka rasa Zamfara da Bayalsa da Rivers da Sokoto.

Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya David Lawal ya koka kan shugabanin jam’iyar sun mayar da mutanen Arewa saniyar ware a jama’iyar APC duk wata kujera dake Arewa da ta fadi ba cike gubinta ba, akwai bukatar APC ta gyara gidanta kamin shiga zabe, in aka yi la’akari da abin da ya faru Bayelsa.

Ya ce yana ta fada wa shugaban jam’iya a gyara domin shugaban jam’iya ba shugaban zartarwa ne ba da zai ce komai ya fadi ya zama doka. Oshiomhole da mukarabansa ba sa aikin da yakamata yakamata a yi maganin lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *