Spread the love

Masana harkokin tsaro na UNREC ta bakinta ta  bayyana cewa,ana shigo da haramtattun makamai kimanin milyan 500 a shiyyar yammacin nahiyar Africa.

Kashi 70 cikin 100 na haramtattun makamai da ake shigo dasu a yammacin nahiyar Africa a Najeriya ake amfani da su, ma’ana kimanin milyan 350 na haramtattun makaman a Najeriya ake jibge su.

 Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani ya nuna gamsuwarsa da kididigar.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa,kimanin haramtattun makamai milyan 1 ne ake amfani da su a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Duk da masana sun jefar da kididigar ta gwamnatin tarayya sun ce ta yi kadan, haramtattun makamai da ke yawo a Nijeriya sun kai dubu 100.

Sun bayyana hanyoyin da haramtattun makaman ke isowa a ƙasar Najeriya, galibi ta iyakokin ƙasashe masu fama da rigin-rigimun ƴan ta’adda, ‘ƴan tawaye ko wasu masu tada tsaune tsaye ne ake shigo da makaman ba bisa ƙa’ida ba, misalin iyakokin ƙasashen LIBYA,MALI,NIJAR,BENIN da kuma ƙasar CHADI. Akwai hanyoyin shigowa na Nijeriya kan iya 1,400 da suke haramtattu.

Masanan sun kuma bayyana cewa, wasu haramtattun makaman na samuwa ne a yayin da ƴan ta’adda suka ci ƙarfin jami’an tsaro,walau ta hanyar bata kashi tsakani ko mamaya,wasu kuma haramtattun makaman,na samuwa ne ga ƴan ta’adda ta hanyar sata.

Hatsaniyar da aka samu Kasar Libiya da Sudan da Tsakiyar Afrika ya karya farashin makaman kana iya sayen AK47 kan dubu 100 ko kasa ga haka. Batagarin suna amfani da Doki da Jaki ta barayin hanyoyi a wurin sayen haramtattun makaman. Masu sayarwa suna sayarwa kowa Boko haram da masu Garkuwa da mutane da masu rikicin addini. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *