Spread the love

 

Daga Bangis Yakawada

A Kaduna Fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu gungun  ‘yan bindiga suka ƙaddamar da farmaki a kan hanyar dake gab da tashar jirgin kasa dake tashi daga Kaduna zuwa Abuja, a unguwar Rigasa.
Jaridar Daily Nigerian, ta ruwaito cewan lamarin ya faru ne a daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, jim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Majiyar mu ta kara da cewa ‘yan bindigan sun yi shirin kwantan ɓauna ne a kan titin na Mando da nufin kai ma duk wanda yabi hanyar farmaki, hangen ayarin motoci da yawa da suka yi yasa suka bude wuta, nan da nan Sojoji da Yansanda suka mayar musu da biki aka yi ta musayar wuta.

Ɗaya daga cikin fasinjojin da harin ya rutsa da su ya bayyana cewa: “Mun yi sa’a sosai Yansanda da Sojoji na kusa damu, har da ministan sufuri Amaechi a cikin fasinjojin, dan dole shi ma ministan ya koma kan hanyar Rigasa.” Inji Musa Lawan.

Da majiyar ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Kaduna, Mohammed Jalige game da lamarin, sai yace ba shi da masaniya, amma zai kara bincike kan abun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *