Spread the love

Kotun ƙoli Nigeria ta sanya ranar Talata mai zuwa a matsayin ranar da zata duba kuma ta sake sauraren ƙorafin da aka gabatar gabanta, game da hukuncin zaɓen jihar Zamfara da Imo dana Bayelsa, alƙalin alƙalan Nijeriya mai shari’a Ibrahim Muhammad Tanko yace idan suka duba suka samu kuskure acikin hukuncin zasu soke hukuncin farko, su dawo kan Wanda ya bayyana gare su.

Korafin ya taso ne daga jam’iyyar PDP da jam’iyyar APC, PDP tana cewa kotun ta yi kuskure data soke zaben ta na jihar Imo, inda aka baiwa APC kujerar a shari’ar, yayin da APC take korafin an tafka kuskure a hukuncin da kotun tayi game soke zaben da APC taci na jihar Bayelsa da miƙa gwamnati a jihar Zamfara ga PDP.
.
Yanzu dai an zuba ido wa jiga jigan alƙalan Nijeriya dake kotun ƙoli su duba batun kuma su fitar da matsayar su ta ƙarshe game shari’o’in uku.

Ba kamar yadda aka saba fadi ba inji Justice Ibrahim Muhammad Tanko cewa Supreme court bata yin kuskure, kuma koda tayi kuskure bata dawowa, yace Wannan maganar ba haka take ba.
.
Matukar kotun tayi kuskure za su soke kuskuren su dawo kan dai dai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *