Spread the love

Wata matar aure mai suna Zainab Sale, wadda ta ce ba ta san shekarunta ba, ta haifi jarirai biyu a manne da juna a gida kuma bayan haihuwar ta ci gaba da zama a gida ba tare da ta ziyarci wani asibitin domin neman shawarar yadda mannannun za su yi rayuwa ba domin tsananin talaucin da ke tattare da su kwana 13 da suka gabata kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Mijin mai jegon, Malam Muhammad Bashir da aka fi sani da Gambo da ke Hayin Kadage a Tudun Wadan  Karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna ya bayyana wa Aminiya cewa shi manomi ne kuma yana sana’ar tura baro, in da ya ce a ranar Alhamis, yana kasuwa sai kanensa ya kira shi cewa ya dawo gida, matarsa ta haifi ’yan tagwaye. Ya ce daga nan ne ya koma gida ya ga halin da yaran suke ciki.

Game da dalilin da ya sa ya bar matarsa ta haihu a gida ba asibiti ba, sai ya ce: “Ba wani abu ba ne illa kawai yadda rayuwa ke gudana, kuma kamar yadda ka sani mu dama ba wai cika damuwa muka yi da zuwa asibiti sosai ba. 

Kusan duk yadda mutum ya kai da ciwo sai dai a yi ta yi masa magani a gida, sai in lamarin ya faskara za a kai asibiti.To, haka ma yawancin duk haihuwa a gida aka fi yi mu a nan, domin wannan ba ita ce haihuwarta ta farko ba, ta farkon ma a gida ta haihu.”

Game da ko matar tasa tana zuwa awo a asibiti Malam Gambo ya ce tana zuwa lokaci bayan lokaci kuma akwai wata mata da ke kusa da su, wacce take zuwa tana duba ta, tana ba ta shawarwari, saboda ta fi saukin kudi.

“Akwai halin matsin rayuwa kuma asibitin wuri ne na kashe kudi, ba-ni-ba-ni ya yi yawa har a kai ga kure mutum. Kuma ka ga wanda duk bai da hali ai dole ne ya nemi sauki wajen Allah. Wannan shi ne dalilin kawai,” inji Malam Bashir.

Game da matakin da zai dauka, ganin cewa an haifi jariran a manne da juna, sai ya ce, “To yanzu dai Allah ne kawai muka sa wa ido, domin babu wani al’amari da zai samu bawa ba tare da sanin Allah ba kuma Shi ne Ya ba mu wadannan jarirai a haka. Don haka shi ne kawai yanzu muke jira Ya yi ikonSa.”

Sai dai ya ce idan zai samu tallafin kudi daga hukuma ko wadansu mutane ko kungiyoyi da za su dauki nauyin aikin raba jariran a asibiti, zai yi na’am da kai su asibitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *