Spread the love

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto

Hukumar zakka da wakafi ta jihar Sokoto,Kamar kowace shekara, cikin shekarru biyar da suka gabata tana amsar  Zakka a  gonar tsohon Gwamnan jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko dake titin Bodinga Sokoto, a wannan shekarar  Shugaban Zartarwar Hukumar  Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sokoto ya Shaidi amsar Zakkar, a Jawabin da yayi , ya bayyana cewa sun zo gonar ne bisa ga gayyatar da aka yi masu daga maigonar cewa lokacin debe zakka ta yi azo a debe hakkin Allah,ya bayyana cewa tun ba yau ba maigonar yayi  Wasiccin cewa da zaran lokacin ya yi aje adebe.

Bisa ga yadda aka Saba anje da wasu malammai da suka hada da Malam Muhammad Dangande Wamakko da Malam Usman Muhammad Dabagin Ardo ,inda Shugaban ya bayyana cewa Mai kula da gonar Malam Bello Gande (Manager) zai yi bayanin dabbobin da ke a gonar,malammai suyi fatawar Abinda za a fitar,  manajan gonar yayi bayani ,malammai sukayi fatawar abin da Shari’a tace a fitar.

An fitar da Shunu ukku da Akuya daya.Shugaban yayi Kira ga sauran masu hannu da shuni,Yan siyasa,ma’aikatan gwamnati, ‘yan kasuwa da sufitar da hakkin Allah, ko su ba da wakafi,kana su bayar ga hukumar Kamar yadda wannan talikin keyi sama ga shekara biyar da suka ga bata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *