Spread the love


Hukumar zabe ta ƙasa ta yi watsi da kiran da shugaban jam’iyar APC Adams ya yi na kar a ayyana ɗan takarar jam’iyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara a jihar Bayalsa.

Shugaban hukumar zaɓe Farfesa Mahmood Yakubu a bayanin da ya yi wa manema labarai a yau Jumu’a ya ce hukumar ta karbi kwafin takardun hukuncin da kotun ƙoli a gudanar a ranar Alhamis da ya nuna zaɓen ya kammala kuma dan takarar PDP ne ke da nasara kamar yadda hukuncin ya bayyana.

Hakan ya kawo ƙarshen furucin Adams na cewa ba wata gwamnati da za a rantsar a Bayesa, hukumar zabe ta bayar da takardar cin zaɓe ga ɗan takarar PDP kowane lokaci za a rantsar da shi domin soma aiki a matakin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *