Spread the love

 
Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.
Shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Mahmud Yakubu, ya tabbatar da hakan a taron manema labaran da hukumar ta gudanar ranar Juma’a a Abuja, babban birnin kasar.

A ranar Alhamis ne kotun kolin kasar ta sauke David Lyon, na jam’iyyar APC, mutumin da a baya INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zabe, saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa INEC takardun bogi lokacin da ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.
Da yake jawabi, Farfesa Yakubu, ya ce Mr Douye Diri na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben, kasancewar mutumin da ya zo na biyu da yawan kuri’u a zaben na watan Nuwamba.
Shugaban na INEC ya kara da cewa Mr Diri ya samu kuri’a 143,172 sannan ya samu kashi 25 cikin dari a kananan hukumomi takwas da aka gudanar da zaben.

sai maganar rantsuwa kamar yadda doka ta tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *